ZAMANI RIGA: BUKIN SAUKAR ALQUR’ANI A TSAKANIN AL’UMMAR HAUSAWA A QARNI NA 21

Authors

  • Abubakar Giwa Aisha Niger State College of Education, Minna, Niger State Author
  • Salihu Hassan Federal University of Education Kontagora Author
  • Tukur Tanko Muhammad Niger State College of Education, Minna, Niger State Author

DOI:

https://doi.org/10.5281/zenodo.14648373

Abstract

Wannan takarda ta tattuna irin sauye-sauyen da zamani ya kawo a al’adar bukin saukar Alqur’ani maigirma. Bincike ya bayyana yadda zamani ya yi tasiri wajen gudanar da wannan buki. Haka kuma bincike ya kawo hidimomin da ake yi wajen gudanar da bukin saukar Kur’ani a cikin al’ummar Hausawa a wannan qarni, tare da nuna yadda ake gudanar da bukin a da.  Binciken ya fito da alfanu ko akasin da wannan sauyin ya haifar a cikin al’ummar Hausawa. Binciken ya yi amfani da dabarar lura tare da hira da tattaunawa da masu ruwa da tsaki wajen tattara bayani don gudanar da wannan bincike. Sannan an halarci wuraren da ake gudanar da wannan buki domin gane wa ido yadda ake gudanar da bukin saukar Alqur’ani a zahiri a cikin al’ummar Hausawa a qarni na 21.  An xora bincike akan ra’in sauye-sauyen al’adun al’umma. Binciken ya fito da irin takalifun da iyaye suke yi a wajen gudanar da wannan hidima da saukar karatun Alqur’ani maigirma. Binciken yana ba da shawara da malamai da iyaye su haxa kai wajen rage xawainiyar hidimomin bukun saukar karatun Alqur’ani.

Downloads

Published

2025-01-23